By Ishaq Dabai
Majalisar dokokin jihar Osun a jiya ta baiwa kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ibadan (IBEDC) wa’adin sa’o’i 48, don maido da wutar lantarki ga al’ummomi shida dake karamar hukumar Ife ta Arewa.
Mazauna yankin sun nuna rashin amincewarsu da rashin wutar lantarki na tsawon watanni biyar, inda suka bukaci gwamnati data shiga cikin lamarin.
Kakakin majalisar Timothy Owoeye, yayin ganawa da wakilan IBEDC karkashin jagorancin shugaban kamfanin na jihar, Mista Akin Ogunleye, yace “Ba za mu iya ci gaba da ganin an jefa mutanen cikin duhu ba tare da neman mafita ga matsalar su ba.
“Gaskiya ne cewa ba alhakin masu amfani da wutar lantaki bane su saya, maye gurbin ko gyara na’urar rarraba wutar lantarki taransfoma, sanduna da sauran kayan aikin da ake amfani dasu wajen samar da wutar lantarki. Ko dai ku gyara taransfoma ko ku maye gurbinsa, ina son a maido da hasken wutar lantarki ga al’ummomin shida cikin awanni 48. ”
Ogunleye, duk da haka, ya yi bayanin cewa rashin wutan lantarki na watanni biyar ya faru ne sakamakon gurɓataccen injin na na’urar rarraba wutar wanda sai mun kashe Naira miliyan 90, lura da cewa kamfanin yana fuskantar ƙarancin kuɗi “kuma ba zai iya ba, a yanzu, ɗaukar cikakken alhakin maido da wutar lantarki ga waɗanda abin ya shafa. al’umma. ”
Kakakin ya dage zaman zuwa ranar 26 ga watan Oktoba domin IBEDC ta fito da samfurin mafita.