Majalisar zartarwa ta tarayya, wato FEC, ta amince da kashe kudi har Naira biliyan 8 domin gina wasu hanyoyi hudu a Nijeriya. Rahotanni sun tabbatar da cewa an ci ma wannan matsayar ne a jiya Laraba bayan taron mako-makon da aka yi a jiya Laraba. A zaman an cimma matsayar ware kudi Naira biliyan 8.2 domin a gina wadannan tituna hudu.
Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana matsayar da aka cin ma a wajen taron nan wannan mako. Wannan ne zama na biyu da sababbin Ministocin kasar sun ka yi. Shugaba Buhari ya amince da wasu takardu hudu da su ka fito daga hannun Ministan ayyuka da gidajen kasar, Babatunde Fashola. Daga ciki akwai batun sake duba kudin wasu kwangiloli.
Za a kuma duba kudin da aka warewa wasu ayyukan da ake yi ne domin ‘yan kwangila su ci gaba da aikinsu ba kakkautawa. Daga cikin inda aka samu canji akwai wajen ginin titin Oba Nnewi Okigwe a Kudu. Haka zalika akwai dogon titin Alace zuwa Garin Ugep da aka karawa kudi saboda canjin da aka samu na farashin kayan aiki daga lokacin da aka bada kwangilar a shekarar 2019 zuwa yanzu. Fashola ya kuma samu amincewar canza dan kwangilar da ake yi aikin gadar Chachangi wanda ta hada Takum da Wukari a Taraba.
Za a kuma taba gadar Garin Katsina a yi mata kwaskwarima. An samu karin kudin da ya haura Naira biliyan biyu na wadannan kwangiloli da aka bada tun tuni. Titin Okigwe zai ci fiye da Biliyan 4 a yanzu, yayin da za a warewa aikin hanyar Ugep Biliyan 11.