Majalisar wakilai ta tarayya ta yanke shawarar shiga tsakani a rikicin da ya barke a fannin sufurin jiragen sama na kasar nan, da nufin warware takaddamar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da wasu kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa.
Sakamakon haka, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da shugabannin majalisar bangarori na zauren sun ce an sanar da su kan sanarwar janye ayyukan da wasu kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suka fitar kwanan nan.
Matasan PDP Sun Bayyana Damuwarsu Akan Rikicin Wike Da Atiku
Magatakardar Majalisar Dokta Yahaya Danzaria ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yammacin juma’ar nan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaban majalisar ya bukaci shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnoli Nnaji da majalisar wakilai da su gaggauta tsaida ranar ganawa da duk masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama da kuma bangaren zartaswa na gwamnati domin lalubo bakin zaren warware matsalolin.
“Shugaban majalisar ya ba da umarnin a gayyaci mutane kamar haka: Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Dakta Zainab Ahmed; Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele; Mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan kasuwanci; da Ministan Sufurin Jiragen Sama, da cewa suma su halarci taron.
“Sauran da ake sa ran zasu bayyana yayin taron sun hada da babban daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA); Wakilin Ƙasa na IATA; Manajan kamfanin Emirates a Najeriya.
Za a sanar da ranar taron ga duk masu ruwa da tsaki da kungiyoyin da abin ya shafa.
A halin da ake ciki, shugaban majalisar ya bukaci dukkanin bangarorin da ke da hannu a lamarin, musamman ma kamfanin jiragen sama na Emirates da su dakatar da duk wani mataki da za su dauka, su kuma jira sakamakon taron.