Majalisar Wakilai za ta gana da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita mai dorewa kan yajin aikin da kungiyar ta shiga.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Yahaya Danzaria ya fitar ranar Litinin din nan a Abuja.
Ya ce taron zai gudana ne a ranar Talatar nan a zauren reshen majalisar wakilai ta Kasa.
Ya ce taron da ASUU da sauran masu ruwa da tsaki za a yi shi ne domin samun mafita mai kan yajin aikin da ASUU ta shiga.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A cewarsa, majalisar ta damu matuka da sabon yajin aikin da aka yi wanda da alama ya bijirewa duk wani yunkuri da aka yi na ganin an magance matsalar.
Ya kara da cewa majalisar ta damu da cewa babu wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami’ar da ke yajin aikin.
KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai Ta Sa Baki Kan Yajin Aikin ASUU
Ya ce majalisar ta fi damuwa da mummunan sakamakon yajin aikin na gaba da kuma ingancin ilimin matasa.
Ya ce an tsare matasa a gida tsawon watanni shida da suka gabata duk da shigar da majalisar da wasu masu kishin Najeriya suka yi akan kari don ganin an shawo kan lamarin.
“Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, ‘Majalissar tana neman wata dama don haduwa da masu ruwa da tsaki da shugabannin ASUU don neman mafita.”
Ya ce hakan ba tare da la’akari da yadda lamarin ya riga ya shiga kotun masana’antu ba.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa, NAN, ya ruwaito cewa ASUU ta kwashe kusan watanni bakwai tana yajin aiki, tun ranar 14 ga watan Fabarairu, bisa zargin da ake yi na cewa ba ta cika ba. Daga cikin bukatun malaman akwai ingantattun kudade da kayan aiki na jami’o’in gwamnatin Najeriya da kuma karin albashi. (NAN)
A wani labarin kuma: An Kama Wani Mutum Da kokon Kan Mutum A Osun – ‘Yan Sanda
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wani matashi dan shekara 28 mai suna Ismail Adewuyi, da aka same shi da kan wata mata da kuma hanji a yankin Ede da ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Yemisi Opalola ta bayyana haka a Osogbo inda ya kara da cewa, an kama wanda ake zargi da aikata tsafi a ranar Asabar a hannun wani dan kungiyar mafarauta ta Najeriya, Isa Usman, wanda ya kai shi wurin ‘yan sanda.