By Abbas Yakubu Yaura
Rikicin mallakar Tony Beach dake yankin Ikang a karamar hukumar Bakassi na jihar Cross River ka iya kawo karshen cece-ku-ce da ake yi a kasar nan ba da dadewa ba bayan shigar da majalisar ta yi.
Majalisar karamar hukumar Bakassi ta karbe ragamar kula da bakin teku nan take.
Idan dai ba’a manta an sha samun tashe-tashen hankula a tsakanin wasu mutane a yankin kan mallakar sa.
An ba da rahoton cewa rikicin ya samo asali ne daga ‘wadanda ya kamata su karbi kudaden haraji da sauran kudade daga kayan amfanin gona da ake jigilar su ta bakin teku.
Binciken ya kuma nuna cewa, an kuma yi ta samun cece-ku-ce kan yadda ya kamata a ba da harajin jiragen ruwa.
Rikicin dai ya yi sanadiyar raunata mutane da dama, lamarin da ya sa jama’a suka firgita tare da yin barazana ga harkokin kasuwancin tekun yankin.
An dauki matakin karbe gabar tekun ne a taron tsaro na majalisar data gudanar a jiya.
Shugaban karamar hukumar, Cif Iyadim Amboni Iyadim ne ya jagoranci taron, tare da halartar dukkan shugabannin sojoji da na rundunar da aka tura yankin.
A cewar jami’an majalisar, taron na da nufin dakile ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi na mutum uku da zai kula da bakin tekun na tsawon kwanaki 90 a jiran sakamakon binciken kwamitin sulhu da tsaro na majalisar domin tantance ainihin mai shi.
Kwamitin rikon wanda yake dauke da Cif Okon Bassey a matsayin shugaba yayin da Mista Bassey Nathaniel da mai ba da shawara na musamman kan zaman lafiya da tsaro, Mista Efffiong Etim Okon, za su kasance mambobin kwamitin.
Daga baya Iyadim ya jagoranci mambobin majalisar tsaro zuwa bakin teku, inda ya bukaci masu gudanar da aiki a wurin da su ba kwamitin rikon kwarya hadin gwiwa.
Sannan ya ce sakamakon farar takarda zai tabbatar da ainihin wanda ya mallaki bakin tekun.
Kazalika ya yi kira ga shugaban kwamitin da ya tabbatar da cewa an tara kudaden shiga daga amfanin gonar dake shigowa ta bakin teku.
Ya kuma yi kira da a samar da kyakykyawan dangantaka tsakanin kwamitin da ma’aikatan bakin teku domin tabbatar da harkokin kasuwanci a yankin ba tare da wata matsala ba.