Majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da ‘yan majalisau biyu bisa zargin alaka da ‘yan fashi.’Yan majalisar – Yusuf Muhammad, Anka mai wakiltar mazabar Anka, da Ibrahim T. Tukur Bakura, mai wakiltar mazabar Bakura – an dakatar dasu na tsawon watanni uku.
A cewar Darakta Janar na Harkokin yada Labarai da Hulda da Jama’a na Majalisar, Mustapha Jafaru Kaura,yace ‘yan majalisar zasu tsaya a majalisar har sai an kammala bincike kan zargin da ake yi musu.sannan “zasu kuma bayyana a gaban kwamitin majalisar akan da’a da alfarma tare da hukumomin tsaro da doka ta basu damar gudanar da bincike a kansu.”
“Wannan wani bangare ne na kudurorin da aka cimma a yanzu a zauren majalisar wanda kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Mu’azu Magarya ke jagoranta, a karkashin al’amuran dake da mahimmancin jama’a cikin gaggawa,” in ji Kaura.
Da yake jagorantar muhawara kan lamarin jim kadan bayan kowane dan majalisa ya yi rantsuwa, mamba mai wakiltar Maru ta Arewa, Honarabul Yusuf Alhassan Kanoma, ya ja hankalin abokan aikin sa kan “rufe batun ” a cikin majalisar, kan manyan zarge -zargen da ake yi wa mambobin biyu.Kanoma yaci gaba da zargin cewa lokacin satar mahaifin mai magana da yawun marigayi Alhaji Mu’azu Abubakar Magarya musamman Yusuf Muhammad Anka da Ibrahim T Tukur Bakura an ce suna ta murna a kan lamarin.
Kazalika ya kuma yi zargin cewa ‘yan majalisun biyu ne suka kashe marigayi Hon Muhammad G. Ahmad (Walin Jangeru), tsohon mamba wanda ya wakilci mazabar Shinkafi a majalisar dokokin jihar.Ya yi ikirarin cewa sun bankado bayanai ta inda ‘yan fashi suka bi diddigin mamacin.inda ya roki hukumomin tsaro dasu bi dukkan layukan wayar su da sauraron duk hirar su.
Da yake yanke hukunci kan lamarin, kakakin majalisar, Rt Hon Nasiru Mu’azu Magarya, ya amince da dakatar da mambobin guda biyu, kakakin Magarya ya kuma umarci shugaban kwamitin da’a da alfarma na majalisar, Hon Kabiru Hashimu Dansadau, da ya gudanar da cikakken bincike kan mambobin. tare da bayar da rahoton abin daya gano ga majalissar.
Comments 2