…Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsawaita wa’adin gwamnatin shugabannin kananan hukumomi da wasu kwanaki a.
Majalisar dokokin jihar Zamfara a ranar Juma’ar nan ta kara wa’adin shugabannin kananan hukumomi da kwanaki 45.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na majalisad Malam Nasiru Biyabiki ya raba wa manema labarai.
KARANTA HAKANAN Majalisar Dokokin Zamfara Ta Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar
Ya ce ‘yan majalisar sun cimma matakin ne a zauren taron bayan sun samu bukatar tsawaita wa’adin aiki daga ranar 14 ga watan Afrilu zuwa 29 ga watan Mayu.
Shugaban majalisar, Farutenure Dosara (na jam’iyyar APC, daga mai wakilatar Maradun 1), ya gabatar da bukatar gwamnati ga majalisar.
Sanarwar ta ruwaito Dosara na cewa bukatar ta fito ne daga hannun Gwamna Bello Matawalle ta ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Kakakin majalisar, Nasiru Magarya, a lokacin da yake mayar da martani kan wannan bukata, ya ce “ya zama wajibi bisa la’akari da muhimmancin da ake da shi, kuma bisa tanadin sashe na 16 (1) da na 17 na dokar kananan hukumomin jihar Zamfara na shekarar 2022.
Bayan tattaunawa da ‘yan majalisar kan lamarin, majalisar ta yanke shawarar tsawaita wa’adin kamar yadda bukatar ta kunsa, in ji sanarwar. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Kebbi: Mun Shirya Tsaf Don Sake Gudanar Da Zaben Ranar Asabar – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC), ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da sake zaben gwamna da na ‘yan majalisar kasa da na jiha cikin nasara a Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa INEC ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu domin sake gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Kebbi da Adamawa da kuma zaben ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jihohi a fadin wasu jihohin kasar nan.