Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom a ranar Talata yayin zamanta ta bayyana kujerun mazabar Esit Eket da Ikono a matsayin wadanda babu kowa bayan da suka fice daga jam’iyyar, PDP zuwa jam’iyyar, YPP.
Kujerun sun kasance karkashin Rt.Hon.Usoro Akpanusoh, mai wakiltar mazabar Esit Eket da Hon. Asuquo Nana Udo, mai wakiltar mazabar Ikono.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Babu Makawa — Inji Kakakin Majalisar Dattawa
Kakakin majalisar Rt. Hon. Aniekan Bassey, yayin da yake Sanarwar kan kujerar, ya ce majalisar ta samu karfinta ne daga sashe na 109 (1) (a-g) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima.
Shugaban majalisar ya ce sashin ya tanadi cewa, “Kasancewar mutumin da jam’iyyar siyasa ta dauki nauyin zabensa na majalisar, ya zama dan wata jam’iyyar siyasa kafin karewar wa’adin da aka zabi majalisar. Matukar dai kasancewar sa na jam’iyyar ba ya samo asali ne sakamakon rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar da yake cikinta ko hadewar jam’iyyun siyasa biyu ko sama da haka ta hanyar daya daga cikin wadanda a baya ya dauki nauyinsa ba”.
Sai dai shugaban majalisar ya umurci magatakardar majalisar, Mrs Mandu Umoren, da ya mika umarnin majalisar ga hukumomin da suka dace.
A halin yanzu, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Barista Aniefiok Dennis (Etinan), wanda ya yi jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar, ya ce “Shugaban majalisar ya dogara ne da tanadin sashe na 109(1) (g) wajen ayyana kujerun ba bu kowa.”
“Ya yi aiki ne da bin doka da oda, tunda ’yan majalissar da abin ya shafa sun yi watsi da kujerunsu, wanda jam’iyyar PDP ta ba su.”
Daga baya an dage zaman majalisar zuwa ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba, 2022, da karfe 10 na safe.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 Da Ake Zargi Da Gudanar Da Wata Haramtacciyar Kwaleji
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da gudanar da wata haramtacciyar kwalejin kimiyyar lafiya a karamar hukumar Bosso ta jihar.
DSP Wasiu Abiodun, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata a Minna.