• Kwamitin majalissar dattijai ya amince da nadin Manjo janar Faruk Yahaya a matsayin shugaban rundunar soji ta kasa.
,Yahaya ya gaji marigayi Ibrahim Gambari ne da ya mutu sanadiyar hadarin jirgin sama a Kaduna.
• Hukumar DSS ta wankeshi daga dukkan zargi.
Majalissar dattijan kasar nan ta tabbatar da nadin Manjo janar Faruk Yahaya a matsayin shugaban rundunar soji ta kasa.
Tabbatar wan na zuwa ne bayan gabatar da rahoton kwamitin hadin kwaiwa na majalissar, da na soji ya yi.
Shugaban kwamitin majalissar dattijai a kan fannin tsaro Aliyu Wamakko ne ya gabatar da rahoton kwamitin.
An dai nada Manjo Janar Yahaya ne a matsayin Mukaddashin rundunar, tun bayan mutuwar marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru sanadiyar hadarin jirgin sama a Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje zai kammala aikin haryar da ya gada
Lokacin da yake gabatar da rahoton Wamakko ya ce,”kwamitin ya amince da dukkannin abubuwan da ake bukatar na zababben” inji shi
Sanatan ya ce nadin Yahaya ya zo, dai dai da amince war sashin na 217 (2abc) na gyararriyar dokar kasar nan, na shekarar 1999.
Kazalika nadin ya zo dai-dai da sashi na 18 daya cikin baka, na tsarin dokar aikin sojin tarayyar Nijeriya, na shekarar 2004.
A karshe kuma ya ce, kwamitin bai Sami wani rahoton dake kalubalantar Wanda aka zaba ba, sannan hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta kwanke shi daga dukkan zargi.