Majalisar dokokin jihar Ogun ta bayar da umarnin kama Goriola Hassan, wanda ake zargi da ayyana kansa da suna a matsayin Olu na Imobi a karamar hukumar Ijebu ta gabas a jihar.
‘Yan majalisar sun kuma umurci hukumomin tsaro da su gabatar da Mista Hassan a gaban majalisar a cikin kwanaki 14 bayan amincewa da kudurin majalisar a ranar Alhamis a Abeokuta.
Kudurin ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi da masarautu ga majalisar wanda shugabanta Bolanle Ajayi ya mika. Daga baya Misis Ajayi ta gabatar da kudirin a amince da shi, wanda Ganiyu Oyedeji ya goyi bayansa, tare da goyon bayan dukkan ‘yan majalisar ta hanyar kuri’ar muryar da shugaban majalisar, Olakunle Oluomo ya jagoranta.
Kamar yadda kwamitin ya lura, Mista Hassan ya mayar da wani ginin gwamnati zuwa zaman kansa kuma ya ki bin umarnin da aka ba shi na ya daina bayyana kansa a matsayin Olu na Imobi. Wanda Kwamitin ya lura cewa ayyukan Mista Hassan na haifar da tashin hankali wanda zai iya haifar da mummunan rikici a cikin al’umma idan ba a dakatar da shi ba.
Kwamitin ya tabbatar da cewa Onitasin na Itasin shi kadai ne Sarkin gargajiya kuma an san shi da mulki a kasar Imobi. Don haka kwamitin ya ba da umarnin cewa al’ummar yankin su karbe gidan da ke unguwar Fotedo, wanda tun da farko Mista Hassan ya ke zaman sirri a ciki.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa Kwamitin ya kuma ba da shawarar a cikin rahoton nasa cewa a bayyana Mista Hassan da ake nema ruwa a jallo, kuma a kama shi, sannan a mika shi ga hukumomin tsaro domin gabatar da shi ga majalisar.
Majalisar, a cikin kudurin ta, ta kuma umarci ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu da ta dauki matakan da suka dace don ganin Mista Hassan ya daina bayyana kansa a matsayin Olu na Imobi. Rahoton kwamitin ya kara da cewa, “Za a iya tunawa cewa tun farko majalisar ta mika gayyata guda uku ga Mista Goriola a ranar 10 ga watan Agusta, 17 ga watan Agusta da 2 ga watan Satumba.
“Ya kasa amsa laifin da mambobin kungiyar zuriyar Imobi, da kungiyar cigaba. Imobi Ijebu, da Baales na kauyuka 36 na Imobi suka yi masa.”