Shugaban jam’iyyar APC na jihar Neja, Haliru Zakari Jikantoro, a ranar Litinin ya gurfana a gaban kwamitin majalisar da ke binciken batar wasu taraktoci 72 na kananan hukumomi 25 dake jihar.
An ce taraktocin an ba da kwangilar su ne ga wani Kafamani mai suna Dogara Ga Allah Ventures domin gyare-gyare a lokacin da shugaban jam’iyyar APCn yake kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018 kuma har yanzu ba a dawo da su ba.
Da yake tsokaci kan kudirin da aka kafa, shugaban kwamitin binciken, Malik Madaki Bosso, mai wakiltar karamar hukumar Bosso a majalisar dokokin jihar, ya ce an gayyaci shugaban jam’iyyar APCn ne, bayan da aka gudanar da bincike kuma aka gano cewa akwai hannunsa kan takardar da gwamnan ya amince da shi wajan bayar da kwangilar sake fasalin taraktocin.
Bosso ya ce kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na yanzu, Abbas Bello, wanda shi ma yayi aiki a ma’aikatar a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Munya Yahuza, guda kuma an gayyace shi sau uku kowanne saboda rawar da ake zargin ya taka a cikin kwangilar amma ya kasa bayyana a gaban Kwamitin binciken.
Gwamnan Arewa Ya Gano Yadda Zai Tsamo Jiharsa Daga Matsalar Tsaro
Ya ce yayin da Bello ya kaddamar da kwangilar a lokacin yana kwamishinan ma’aikatar, ana zargin tsohon shugaban karamar hukumar Munya da karbar tarakta uku daga hannun dan kwangilar.
Dan majalisar ya ce bayan gayyatarsu sau uku kowanne, za a tilasta wa kwamitin yin amfani da sashe na 129 na kundin tsarin mulkin kasar tare da bayar da sammacin kama su.
Anashi bangaren Shugaban jam’iyyar APC, Haliru Zakari Jikantoro, ya ce an fara cinikin ne a watan Afrilun shekarar 2016 kafin a nada shi kwamishina a watan Disambar shekarar 2016.
Jikantoro ya ce a karshe ya gana da shugaban ALGON na wancan lokacin wanda ya ce ya makara, marigayin ya umarce shi da ya janye kwangilar saboda karancin kudi don gudanar da aikin gyaran.
Ya ce babu wata takarda a hukumance tsakaninsa da dan kwangilar na kowane salon biyan kudi har sai ya da ya bar ma’aikatar a shekarar 2018.
A baya dai kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya NULGE ta rubutawa majalisar dokokin jihar cewa ta binciki inda taraktoci 72 na kananan hukumomi 25 da suka bata.
NULGE a wata wasika da ya aike wa kakakin majalisar ta yi zargin cewa ma’aikatar kananan hukumomi a shekarar 2016 ta umurci kananan hukumomi 25 da su mika tararaktocinsu guda uku kowannensu ga dan kwangila domin gyara, wanda suka yi amma bayan shekaru shida ba a ga taraktocin ba. Kuma ba a yi wani bayani kan inda suke ba.