Majalissar Dokokin jihar Fulato ta bayyawa Gwamnan jihar Simon Lalong makwanni biyu da ya kawo karfe matsalar tsaro dake ciwa jihar tuwo a kwarya.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalissar Philip Dasun ne ya bayyana matsayar yan majalissar, lokacin da yake zanta wa da manema labarai a garin Jos.
Mr Dasun ya ce, Majalissar ka iya bayyana matsayar ta, da kuma matakin da zata dauka idan makwani biyun sun cika.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Mun karbi tuban Sadiya Haruna” inji Hisba
“A matsayin mu na yan majalissa masu wakiltar al’uma, Muna Kira ga mutanan jihar Fulato da su yadda damu bisa irin jajircewar mu” inji shi.
” Mun bai wa Gwamna makonni biyu da ya dauki mataki wurin kawo karshen tashin-tashina a jihar” a cewar shi.
“Muna kira ga gwamna Simon Bako Lalong, da ya fito da wata matsaya da za ta kare mu a matsayin mu na al’umma, domin samun ci gaba da sadaukar da Kai, ga jihar Filato.
Kazalika Shugaban kwamitin ya kuma yi kira ga Sarakunan Gargajiya dake fadin jihar, da su ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro da bayanai yankunan su, domin kare rayukan al’umar jihar baki daya.
A karshe ya shawarci Sarakunan da su karfafawa jami’in Sakai a yankunan su, domin tallafawa wajan kare rayukan mutanen jihar.