kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a ranar Talata ya gayyaci ministar kudi, kasafin da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed da ministan ilimi, Adamu Adamu, kan sanarwar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) zasu yi.
A ranar Litinin ne kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani idan gwamnatin tarayya ta ki cika alkawuran da ta daukarwa kungiyar kamar yadda yake kunshe a cikin yarjejeniyar fahimtar juna.
Bayan majalisar ta amince da kudirin da Julius Ihovbare ya gabatar, Gbajabiamila ya jaddada cewa dole ne a fitar da kudade ga jami’o’i.
Ihovbare ya ce da alama gwamnatin tarayya ba ta son mutunta yarjeniyoyin da ta rattabawa ASUU a watan Disamba na 2020.
Ya ce: “Gwamnatin tarayya ba ta fito ba, kuma ba ta dora wani mahimmanci ga bukatar gaggawa da sake mayar da fannin ilimi daidai da manufofinmu na cigaba.”
Da take goyon bayan kudirin, Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abia) ta ce kamata ya yi gwamnati ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta da kuma cika yarjeniyoyin da ta cimma da ASUU.
Babban Alkalin Majalisar, Muhammed Tahir Monguno (APC, Borno) ya ce ya kamata majalisar ta duba yiwuwar kara kasafin kudin fannin ilimi.
Uzoma Nkem Abonta (PDP, Abia) ya ce yin wasa da manyan makarantu wani shiri ne na rashin tsaro da rashin zaman lafiya.