Hukumar dake kula da harkokin ilmi ta kasar Ghana GES ta umarci makarantar sakandaren Mata ta Wesley Girls High School da ma sauran Makarantun sakandare da su bar dalibansu su sakata su wala dangane da ibadar su ta wayan Ramadan.
Hukumar ta bada wannan umarni ne a ranar Asabar 1 ga watan Mayu cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun Kakakin ta Madam Cassandra Twum Ampofo.
Makarantar Sakandaren ta Wesley Girls High School ta haramta wa dalibanta Musulmi gudanar da azumin watan Ramadan, to sai dai haoan ya janyo mata kaicho gurin yan kasar da ma Kungiyoyin kare hakkin Bil’adama.
Ko da yake ta ce ta yanke shawarar haramta azumin ne lura da irin halin lafiya da daliban ka iya fadawa.
Amma sanarwar ta Hukumar GES ta bukaci Makarantar da ta tashi tsaye ta dauki matakin kare aukuwar hakan ba wai haramta musu azumin.
Sai dai ta ce duk dalibin da ya dauki azumi kana wani al’amari ya faru da shi, to lallai ya kuka da kansa domin babu ruwan Hukumomi.