Sakamakon kawo karshen rike mukamin Rijistira Makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake Nasarawa a jihar Nasarawa da Hajiya Fatima Sabo ta yi bisa mukamin Kwamishiniyar Ilimi da gwamna A.A Sule na jihar ya ba ta, Alhaji Munir Ahmad ya zama sabon Rijistirar makarantar.
Munir, wanda yake dan garin Zariya ne dake jihar Kaduna, ya yi digirinsa na farko a bangaren sanin sha’anin shugabanci daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, sannan ya yi digirinsa na biyu a bangaren sanin sha’anin al’umma da shugabanci daga Jami’ar Bayero dake Kano.
Kafin nada shi a wannan mukamin, Alhaji Munir ya kasance ma’aikaci ne a Kwalejin Ilimi ta gwamnatin tarayya dake Zariya, inda ya rike mukamai daban-daban a matakai mabambanta.