• Makarantar nazartan aikin shari’a ta saki sakamakon jarabawar 2021.
• Wasu da dama sun fadi jarabawar.
• inda wasu kuma suka ki zama rubuta jarabawar.
A kalla Mutum 1,325 suka yi rashin nasara a jarabawar karshe na zama cikakken lauyoyi a Nijeriya, na shekarar 2021 wanda aka saki sakamakon a jiya Talata.
Kamar yadda hukumar kididdiga ta ilimin shari’a ta fitar cewa, Mutum 5,770 ne suka zauna rubuta jarabawar na wannan shekarar
Kazalika mutun 1,326 da suka fadi jarabawar ya nuna cewa sun kai kashi 22.98 cikin dari kenan, na wadanda suka zauna jarabawar.
Ya yin da Mutum 20 cikin su, Wanda ya kai kashi 0.007 cikin dari, suka sami Sakamakon Mafi darajar wato (Fist class). Inda mutun 2,172, kashi 37.64 kenan cikin dari suka sami sakamoko Mai darajar ta biyu wato (Upper Credit). Wadanda suka sami sakamakon mai darajar ta uku kuwa, sun kai Mutum 1,725, kaso 29.90 kenan ciki dari, kamar yadda hukumar ta bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jirgin yankin da Nijeriya ta siyo sunfara isowa
Kazalika a karshe mutun 35 suka sami sakamakon Fass, da ya kai kashi 0.61 cikin dari, inda kuma mutum 60 da su kai kashi 1.04 cikin dari, suka ki zama rubuta jarabawar.
Comments 1