Manchester City ta rage yawan tazararar da ke tsakaninta da Liverpool a teburin Premier wadda ke saman teburi bayan ta lallasa Aston Villa da ci 3-0 a filin wasa na Etihad.
Sai dai Liverpool ka iya kara girman tazarar na maki shida idan ta doke Tottenham a gobe Lahadi a wasan mako na 10.
Duk da dai ta ci wasan tare da wasa mai kyau, sai daga baya ne Man City ta samu damar keta bayan Villa din, inda suka wahalar da City a zagayen farko na wasan.
Amma kokarin nasu ya kare ne dakika 20 kawai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Mai tsaron raga Ederson ne ya bugo kwallo ga Gabriel Jesus, shi kuma ya bai wa Sterling wanda bai yi wani jira ba ya shiga yadi na 18 kuma ya dada ta cikin raga a minti na 45.
A minti na 65 Kevin De Bruyne ya kara ta biyu, minti biyar bayan haka kuma Gundogan ya kara ta ukun.
Yanzu maki uku ne tsakanin City wadda take mataki na biyu da kuma Liverpool wadda take saman teburi.