Daga Sulaiman Musa
Wasu da ake zargin Fulani Makiyaya ne a safiyar yau din nan suka kashe wasu manoma ‘yan kabilar Tiv a wani sabon harin da suka kaddamar a kauyuka uku da suke karamar hukumar Doma a cikin jihar Nasarawa.
Kauyukan da aka kai wa harin sun hada da Ajikamaka, Gidan Rail da kuma kauyen Ankoma da ya yi iyaka da jihar Nasarawa yankin da mafi yawansu ‘yan kabilar Tibi ne.
Wadanda harin ya shafa an nakalto cewa suna cikin barci ne maharan suka farmakesu, inda suka kunna wa gidajen wuta yayin da kuma mazauna kauyuka suka arci na kare domin neman tsira da rayukansu.
Wadanda aka kashe din su ne Tsekaa Chiatyo, Kwaghdoo Tsekaa, Sewuese Tsekaa, Bobo Chiatyo, Aondosee Fidelis, Aboy, Igba Aduku, Iwuesi da kuma Aseer.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Doma, Hon. Atukpa Asukunu ya tabbatar da wannan harin da aka kai.
Jami’in watsa labaran ‘yan sandan Nasarawa, ASP Ramham Nansel ya ce har zuwa lokacin da aka tuntubesa ba a kawo musu rahoton wannan harin a shalkwatarsu ba.