Daga Sulaiman Musa
A daidai lokacin da Nijeriya ta samu sabbin wadanda suka kamu da cutar Korona a Nijeriya, an wayi gari sama da mako guda babu wanda cutar ta kashe a kididdigar da hukumomi suka fitar a ranar Litinin.
A ranar Litinin din aka kawo zuwa mako guda cif da cutar ba ta jijjiga wani balle ta kashe ba a daidai lokacin da mutum sama da miliyan 3 suka rasa rayukansu a duniya da kuma sama da mutum 2,000 da cutar ta kashe a Nijeriya tun lokacin da cutar ta barke zuwa yau.
Hukumar NCDC a bayanan da take fitar na kullum-kullum, ta bayyana cewa ana samun saukin kamu da cutar kana ana cigaba da daukan matakan da suka dace na kula da cutar.