Babban mai kula da Cibiyar Bishara ta Duniya ta Dunamis, Fasto Paul Enenche ya ce zaben 2023 ya wuce na zahiri ya koma zuwa na tsafi.
Fasto Eneche da yake magana a yayin taron hadakar cocin sa na watan Janairun 2023, a Glory Dome da ke Abuja a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, ya bayyana cewa makomar Kiristoci na cikin hadari a zaben 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Jirgin Kasan Edo
Malamin ya kuma bukaci mabiya cocinsa da su tabbatar sun samu katin zaben su na dindin PVC.
Yace;
“Ka kira ‘yan uwanka ka gaya musu, idan suka zabi masu kisan kai, Allah zai hukunta su.
“Na sake cewa, idan suka zabi ‘yan ta’adda da masu daukar nauyinsu, masu jihadi, Allah zai hukunta su.
“Saboda wasunsu a kauyuka, ba su san abin da ke faruwa ba saboda ba sa cikin kafafen sada zumunta.
“Najeriya na kan wani yanayi da dakarun barna dake son wargaza ta amma ina gaya muku cewa al’ummar nan za ta cika ajandar Ubangiji.
“Ka kira ‘yan uwanka ka gaya musu wanda za ka zaba, da yadda za su kada kuri’a. Ina fadin haka ne saboda batun zaben a yanzu ba na zahiri ba ne, ya koma na tsafi.
“Ruhin al’umma ce kuma makomar cocin Yesu a Najeriya.
“Kaddarar Kiristoci tana cikin hadari a nan don haka kada ku kalla kuma ku yi shiru. Ina son kowa ya yi magana ya gaya wa wasu abin da za su yi. ”
A wani labarin kuma, Ziyarar Buhari: Gwamnatin Yobe Ta Ayyana Ranakun Hutun A Jihar
Gwamnatin jihar Yobe ta ayyana ranakun Litinin 9 da Talata 10 ga watan Junairu, 2023 a matsayin ranar hutu yayin da shugaba Buhari ya kai ziyara jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 8 ga watan Janairu, 2023, kuma mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jiha, Alhaji Garba Bilal.