Wani matashi mai Mustapha Adamu ya guntule hannun wani makwabcinsa mai suna Adamu Mohammed, ta hanyar amfani da adda wajen sare hannun yayin da wata takaddama ta shiga tsakaninsu, kamar yadda majiyarmu ta rawaito.
Wannan mumunan al’amari ya faru ne a Unguwar Gede dake cikin garin Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda wani mazaunin unguwar, Ibrahim Salihu ya tabbatar.
Salihu ya ce rikicin ya auku ne a sakamakon wani sa’insa da aka samu tsakanin Adamu Muhammad da aka sare ma hannu da wasu gungun matasa yan wiwi a Unguwar Gede a makon da ya gabata.
A cewarsa, rikicin ya samo asali ne a daidai lokacin da Adamu Muhammad ya gargadi matasan da su daina shan tabar wiwi a unguwar Gede, ashe wannan gargadi bai yi ma matasan dadi ba, inda suka fara dambe da shi.
“Daga wannan shawarar ne sai matasan suka fara fada da shi, amma Adamu Muhammad ya doki guda daga cikin matasan da icce a kai, inda shi kuma nan take Mustapha ya zaro adda daga cikin rigarsa ya cizge ma Adamu hannu.
“Ganin haka yasa jama’a suka taru da nufin kama Mustapha don mikashi ga Yansanda, amma zakara ya bashi sa’a ya ranta ana kare, kuma ya tsere.” Inji shi.
A yanzu haka Adamu yana kan gadon asibitin koyarwa na jami’ar Abuja yana samun kulawa, tuni shugaban karamar hukumar Gwagwalada Alhaji Kassim Mohammed ya kai masa ziyara don ganin halin da yake ciki.
Shi ma DPO na Yansandan Gwagwalada ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce yaron ya tsere, amma suna bin sawunsa domin samun nasarar kama shi.