By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar rejistar malamai ta kasa (TRCN) a ranar Asabar ta ce adadin malamai guda 9,204 ne suka shiga jarrabawar tantancewar kwararru da aka gudanar a fadin kasar, in ban da jihohi biyu.
Darakta mai rikon kwarya da bayar da lasisi na TRCN, Dokta Jacenta Ogboso, wadda ta bayyana hakan ta ce majalisar ta mayar da jadawalin jihohin Sokoto da Zamfara saboda matsalolin tsaro da suka addabi yankin a baya-bayan nan.
Da take jawabi a Abuja yayin da take kula da jarabawar a Maitama, Ogboso ta bayyana cewa ‘yan takara 125 ne suka yi rajista a Sokoto da 151 a jihar Zamfara.
Sannan ta kara da cewa za a gudanar da jarabawar a jihohin biyu ne idan matsalar tsaro ta inganta a jihohin.
Akan magance munanan ayyuka a wajen gudanar da atisayen, ta ce TRCN ta bullo da wani tsari na tantancewa ta hanyar wani dandali na sashen ICT daya bullo da shi domin gano ainihin mutanen da suka yi rajista domin yin jarrabawar don gujewa kwaikwayar ’yan takara.
Ogboso ta bayyana cewa an rage yin jarabawar zuwa sau biyu a kowace shekara sakamakon raguwar aikace-aikacen da ake yi, inda ta kara da cewa karuwar aikace-aikacen da aka samu tun da farko a kololuwar PQE ya biyo bayan gaggawar cika wa’adin aiwatar da manufofin gwamnati na tabbatar da hakan.
ƙwararrun malamai ne kawai ke cikin tsarin makarantarta.
Tun da farko, babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Mista David Adejo, wanda shi ma ya sa ido a kan aikin, ya ce malaman da ba su yi rajistar rubuta PQE ba ba malamai ba ne a Najeriya.