Malaman Jami’a guda biyu wanda ya hada da Adamu Chonoko na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya da kuma Umar Chonoko Kwalejin kimiyya da fasaha dake Kaduna, wadanda aka yi garkuwa da su kwana 10 da ya gabata sun yi nasarar kubcewa daga hannun masu garkuwa da jama’ar.
Kakakin kungiyar Kebbi mazauna garin Kaduna, kuma Garkuwan Wakilin Sarkin Zurun Kaduna, Garba Muhammad shi ne ya tabbatar da wannan lamarin a ranar Lahadi.
Garba ya bayyana cewa; wadanda suka samo suka gudu din dukkaninsu ‘yan jihar Kebbi ne, kuma ‘yan’uwan juna ne. “’yan’uwan kuma ‘yan asalin jihar Kebbi sun yi nasarar tserewa ne daga hannun masu garkuwa da su, inda suka iso fadar Wakilin Sarkin Zurun Kaduna, kuma sun samu tarbar daga Wakili da misalin karfe 11:51 na safiyar ranar Lahadi. Muna godewa Allah da wannan tseretarwar.” In ji shi.
A cewarsa, Chonoko ya tafi kai naira miliyan biyu ne da mota domin biyan kudin fansar dan uwansa Adamu, amma sai masu garkuwa da mutanen shima suka rike shi suka nemi kuma karin kudi har naira miliyan biyar. “An kara musu miliyan 3, wanda ya zama naira miliyan biyar ke nan, amma masu garkuwa da mutanen suka sake neman a kara musu naira miliyan 10. Amma bukatarsu ba a samu an biya ba, kawai da safiyarnan tare da taimakon jami’an tsaro, suka samu suka tsere.” Ya tabbatar.
Ya mika godiya ga kafafen watsa labarai, da kuma jami’an tsaro da dukkanin wadanda suka taimaka da addu’o’i har suka samu wannan ‘yancin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da lamarin. Inda ya ce rundunar sun samu labarin ‘yancin da suka samu daga wurin iyalansu.