Mataimakin shugaban Jami’ar Ibadan wato Farfesa Idowu Olayinka ya mika ma’aikatan Jami’an guda shida ga jami’an tsaron farin kaya wato DSS bisa zarginsu da magudin jarabawa. Ma’aikatan na aiki ne a sashen DLC.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya tabbatar da cewa an kama su ne a ranar Juma’a, inda DSS din suka ajiye su a wurin ajiye mutane a hukumar DSS, kafin daga bisani a ranar Litinin aka sake su bisa sharadin da hukumar Jami’ar ta nema.
Bincike ya tabbatar da cewa ma’aikatan sun rika satar takardar jarabawar suna isa da shi dakin jarabawa da sauran laifuka makamantan wadannan.