Kungiyar malaman jami’o’in ASUU reshen jihar Kaduna (KASU) ta ki komawa karatu duk da barazanar da gwamnan jihar Nasir El-Rufai na korar su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, hukumar gudanarwar makarantar ta bukaci daliban da su koma karatu domin jarrabawar su bayan barazanar da gwamnan ya yi na korar su.
Dangane da abubuwan da suka gabata, an ga wasu daga cikin daliban a ajujuwa suna rubuta jarabawarsu a ranar Litinin karkashin kulawar shugaban jami’ar da sauran ma’aikatan cibiyar.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa , mambobin kungiyar malaman jami’o’i na kasa wato (ASUU) reshen jami’ar sun ki shiga cikin aikin kulawar, su na masu cewa, yajin aikin na ci gaba da gudana don haka ba za su shiga aikin jarrabawar ba.
Babu wanda ya isa ya ba mu umarni – Museveni ya fadawa Amurka
Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar a wata sanarwa da ta fitar a karshen taronta a jami’ar Kaduna da ya gudanar a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce an samu kura-kurai a lokacin jarrabawar.
Shugaban kungiyar ASUU – reshen KASU, Kwamared Peter Adamu da Comrade Usman Abbas, sakataren kungiyar ne suka sanya wa sanarwar hannun.
Duk da haka Sanarwar ta yi kira ga ƙungiyar da ta tattara dukkan laifuffukan da aka samu a cikin jarrabawar da aka yi sannan a tura su ga hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa.
A nasa martanin, Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Ashafa, ya ce, kungiyar ASUU reshen Jami’ar na goyon bayan Jami’o’in Tarayya ne kawai, Amma ba su da wata matsala kai tsaye da Gwamnatin Tarayya da ya jawo yajin aikin.