Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta fara yajin aiki a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, ta dauki rayukanmalaman jami’ar Calabar 10, ciki har da wasu Farfesa.
Daily Post ta ruwaito cewa, Shugaban ASUU na jami’ar wato UNICAL, John Edor ne ya tabbatar da hakan a yau Laraba a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya musanta rade-radin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa adadin ya kai 21.
KARANTA WANNNA LABARIN: Ana Fargabar Yan bindiga Sun Sace Fasinjoji A Babban Haryar Kaduna
“Ba daidai ba ne cewa mambobin kungiyarmu 21 a Jami’ar Calabar sun rasa rayukansu a sakamakon ci gaba da yajin aikin ASUU a fadin kasar nan.
“Zan iya tabbatar da cewa mun rasa kusan mambobinmu 10 amma ba duka Farfesa ba ne. Farfesan sun hada da Gabriel U. Ntamu, Judith Otu, Udosen, Kate Agbor, Obia da sauran malamai.”
Ya ja hankali kan abin da ya bayyana a matsayin rashin kulawa da tursasawa da gwamnatin tarayya ke yi inda ya sha alwashin ba za su yi watsi da bukatarsu ba kafin su janye yajin aikin.
“Duk da cewa gwamnati ta ki sauraron halin da muke ciki tare da samar da ingantacciyar hanya ba tare da cikas ba, za mu ci gaba da tinkarar duk asarar da muka yi ba tare da la’akari da hakan ba. Muna sane da yunwa, tsoratarwa ko umarnin kotu. Ba mu hakura da wannan fafutukar na mu ba. Za mu kai har ƙarshe tare da samar da mataki mai ma’ana inda aka yi abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi. ” Ya cewarsa.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamnoni Dake Goyon Bayan Wike, Sun Kauracewa Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Jam’iyar PDP
Biyo bayan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, gwamnonin a dake goyon bayan gwamnan Rivers Nyesom Wike a ranar Laraba sun kauracewa taron kaddamar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar a hukumance.
Daily Post ta ruwaito cewa, Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom na jihar Benue; Seyi Makinde na jihar Oyo; Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu; Okezie Ikpeazu na jihar Abia da shi kanshi gwamna Wike