Malamai 150 daga Kwalejin ilimi ta jihar Kuros Ribas da kuma Kwalejin lafiya ta jihar a yau Laraba ne suka gudanar da zanga-zanga a garin Kalaba, inda suka yi kira ga gwamnati da ta yi gaggawar maida su wuraren ayyukansu tare da kiran da a biya su albashinsu da aka ki biyansu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Malaman wadanda aka kora sun gudanar da zanga-zangar ne a gidan gwamnatin jihar, inda suke dauke da Alluna da suke nuni da gwamnati ta maishe su wuraren ayyukansu tare kiran da a biya su albashinsu da aka rike na watannin Satumba da Oktoba.
Malaman sun yi korafin cewa an kore su daga wuraren ayyukansu ne ba bisa ka’ida ba. Da yake bayani a madadin masu zanga-zangar Emmanuel Nyador, Sakataren kungiyar Malaman Makarantun kimiyya da fasaha ta Nijeriya, ya ce ba su amince da hukuncin da gwamnatin jihar ta dauka ba.
Nyador ya shaidawa shugabancin majalisar jihar cewa; wadanda suke cikin zanga-zangar sun hada da Malaman Kwalejojin ilimi, Malaman Makarantun kimiyya da fasaha. Inda ya ce sannan akwai Malamai 150 daga Kwalejin ilimi da kuma Kwalejin lafiya wadanda aka kora ba bisa ka’ida ba sannan aka hana su albashinsu har na tsawo wata biyu, inda ya kara da cewa; sannan aka cire sunayensu cikin jerin wadanda za a rika biya albashi.
Da yake mayar da bayani, Kakakin majalisar, Eteng Jonah-Williams, ya ce majalisar za ta kafa kwamiti da zai yi duba ya zuwa ga korafinsu, inda za su tattauna da shugabancin kungiyar domin ganin an yi sulhu mai dorewa da za a gabatarwa da gwamnan cikin mako guda.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; ko a jiya Talata ma 6 ga watan Nuwamba, sama da Malamai 500 na makarantar kimiyya ne suka gudanar da zanga-zanga suma a ofishin gwamnan jihar, inda suke neman da a maishe su wuraren ayyukansu tare da biyansu albashinsu da aka danne.