Awanni 48 bayan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i Najeriya ASUU ta ayyana wata ɗaya yajin aikin gargaɗi, Malamai a Kwalejojin Ilmi na Kasar nan, sun yi barazanar cewa bazasu gajiya ba, domin bin bayan takwarar su ASUU dake yajin aiki a halin yanzu.
Malaman, a ƙarƙashin Ƙungiyar Malaman Makarantun Kwalejojin Ilmi ta Najeriya (COEASU), sun ce nan da wasu satittika zata kira Babban Taro na Majalisar Zartaswa na Ƙasa domin ɗaukar matakai idan Gwamnati bata yi wani abu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abba Kyari: Bamu ɓoye kowa da yake da hannu a shigowa da hodar Iblis — NDLEA
Dayake jawabi ga Manema Labaru a Abuja, Shugaban Ƙungiyar COEASU Smart Olugbeko ya bayyana rashin jindaɗi na halin ko in kula na Gwamnatin Shugaba Buhari wajen cika alƙawurran data ɗauka da Ƙungiyoyi, wanda ya nuna cewa Gwamnati tana rashin kula akan rikici a ɓangaren ilmi.
Olugbeko ya lissafo wasu al’amura na tattaunawa a yarjejeniyar shekarar 2009, wanda rikicin da tsarin biyan Albashi na IPPIS ya janyo, sakin Naira biliyan 15 kuɗin gyaran makarantu wanda a cewar su suka hana cigaban ilmin Kwalejojin Ilmi a Najeriya da sauran su.
“Ƙoƙari da kungiyoyi suka yi na sanyawa Gwamnati ta cika alƙawurran ta har yanzu kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba.