Malaman Makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati a babban birnin tarayya (FCT) a karkashin inuwar kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki 5 daga yau.
Sun Yi hakan ne domin nuna rashin Jin dadin su dangane da biyansu bashin karin girma na ariyas-ariyas.
Da take yi wa manema labarai jawabi a karshen taron gaggawa na kungiyar zartaswar a Gwagwalada, mukaddashin sakatariyar kungiyar Kwamared Margareth I. Jethro, ya ce kungiyar ta yanke shawarar fara yajin aikin ne saboda rashin jajircewa na shugabannin kananan hukumomi shida za su daidaita haƙƙin malaman firamare na LEA a yankin.
Ta ce duk da wa’adin da aka bai wa shugabannin majalisun a baya na su biya hakokin da suka hada da rashin aiwatar da karin girma a shekarar 2019 da 2020 a wasu makarantun Gwamnati, sun ki amsa kiran kungiyar.
Ta Kuma Kara da cewa, shuwagabannin kansilolin sun kuma ki biyan basussukan karin girma ga malamai daga shekarar 2014 zuwa 2018, da na shekara ta 2020 da 2021 da kuma inganta kwararrun malamai.
Ta kuma ce gwamnatin babban birnin tarayya Abuja ta gaza biyan malaman makarantun sakandire bashin ariyas-ariyas na shekarar 2016, 2017 da 2018 duk da wa’adin da suka bada a baya.
Jethro ta yi gargadin cewa idan har hukumar babban birnin tarayya Abuja da shugabannin kananan hukumomi shida suka kasa biyansu hakkokinsu a cikin kwanaki biyar na yajin aikin gargadi, malamai a babban birnin tarayya za su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
Shugaban karamar hukumar Gwagwalada kuma shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen babban birnin tarayya Abuja, bai amsa kiran waya da aka yi masa ba ko kuma amsa sakonnin kartar kwana da aka aike ta wayar salular sa, kan lamarin.