Wata malamar makaranta mai soyayya da ɗalibin da ta taɓa koyarwa a makarantar firamare ta janyo cecw-kuce a yanar gizo.
Mutanen sun san da labarin soyayyas su ne bayan ta sanya wani bidiyo a TikTok, inda ta nunawa duniya shi sannan ta bayar da tarihin abinda ya faru tsakanin su a baya. Rahoton Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Ramadan: Buhari ya aika wani saƙo ga musulmi yayin da za’a fara azumi
Budurwar mai amfani da sunan, @_blackbird_01, ta sanya tsofaffin hotunan su inda ta rubuta:
“Daga malamar makaranta a firamare zuwa masoya.”
A ƙasan bidiyon kuma sai ta rubuta:
“Na raine shi har na jira girman sa.”
Mutane da dama sun sanya shakku kan labarin nata yayin da wasu suka ƙarya ta, amma budurwar ba ta damu da ko ɗaya ba.
Ta ba wasu amsa da cewa:
“Mutane suna nan suna ta gutsiri tsoma kamar wani sabon abu ne. Na ji dadi cewa nayi hakan kuma ban da wata nadama.”
Ga kaɗan daga cikin sharhin da mutane suka yi waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
KRATUS ya rubuta:
“Wannan ƙanin ni ne meyasa baku ɗauKi hoto a cikin aji ba.”
SAMMY PRAIZE ya rubuta:
“Wannan labarin akwai lauje cikin naɗi ko dai nine bangane ba.
oyinlola ta rubuta:
“Ban gane ba wai menene yake faruwa a nan ne.”
TIKTOK ya rubuta:
“Yayar shi ce ke babu wani abin da zaki gayamin.”
‘Yar Albarka: Bidiyon Yadda Wata ‘Yar Aiki Ta Gyara Gidan Iyayenta Ya Girgiza Intanet
Labarin yadda wata ƴar aiki ta taimaki rayuwar iyayen ta ya sanya mutane da dama sun ƙara ɗaukar himma.
Budurwar ta bayyana yadda ta taso cikin wahala aka haife ta cikin gidan ƙasa ta yadda ta bar gida bayan ta kammala karatun firamare.