Babban Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami SAN ya nesanta kansa daga zargin da ake cewa da sa hannun wasu jami’an tsaro suka je gidan mai sharia Mary Odili domin gudanar da bincike.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan kan kafafen yada labarai Dr Umar Jibrila Gwandu ya fitar, ya ce wannan kawai wata makarkashiya ce da ake shirin kullawa ministan, a dan haka tuni ya bayar da umarnin bincikar ƙawanyar da jami’an tsaron suka yiwa gidan mai shari’ar.
Ya kuma kara da cewa yana da kyau al’ummar kasa su fahimci cewa babu wani kwamiti da aka samar karkashin ofishin antoni janar na kasa da nufin bibiya tare da kwato wasu abubuwa da ake tunanin sun saba da ka’ida.
Maimakon hakan karkashin ofishinsa akwai kwamitin ministoci da kan tattara sakamakon kadarorin da aka kwace tare da aiwatar da mataki na gaba.