By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan sanda a kasar Malawi sun harba barkonon tsohuwa a ranar Juma’a a kan mutane masu gudanar da zanga-zangar kusan 10,000 a babban birnin kasar Lilongwe na nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma cin hanci da rashawa a birnin, kamar yadda wakilan AFP suka gano.
“Abin kunya ne a tsarin dimokuradiyya, mun sami izinin yin zanga-zanga,” in ji daya daga cikin shugabannin kungiyar wanda tsohon dan majalisa ne, Bon Kalindo.
Rundunar ‘yan sandan ta ce ba a sanar dasu abubuwan dake faruwa a kasa ba, kuma sun kasa cewa komai kan lamarin.
Sai dai Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin kananan hukumomi suka koka kan tsadar rayuwa da kuma halin ko in kula da gwamnati ke yi kan halin da ‘yan Malawi ke ciki.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kasar Malawi na daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, inda kashi 11% na al’ummar kasar ke amfani da wutar lantarki.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga shugaba Lazarus Chakwera da ya cika alkawuran yakin neman zabensa na samar da ayyukan yi miliyan daya da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.
Zaben da aka yi a shekarar 2020 na tsohon madugun ‘yan adawar, wanda ya yi tir da tabarbarewar tattalin arziki da cin hanci da rashawa na gwamnatin magabacinsa Peter Mutharika, ya haifar da kyakkyawan fata a wannan karamar kasa ta kudancin Afirka.
Masanin kimiyyar siyasa dan kasar Malawi Michael Jana da ke Afirka ta Kudu ya yi gargadin cewa “Akwai rashin jin dadi gaba daya,” wanda ya nuna cewa babu wani shirin farfado da tattalin arziki da gwamnati ta fara.
Masu zanga-zangar sun baiwa gwamnatin kasar wa’adin kwanaki 14 domin ta amsa bukatunsu ko kuma su sake fitowa kan tituna.
Comments 1