Kasar Mali ta kasa biyan kusan dala miliyan 80 da ake bin ta, bayan takunkumin da aka kakaba mata a watan Janairu ya toshe asusun ajiyarta na bankunan kasashen waje.
Jimillar bashin da ake bin kasar tun watan Janairu ya kai dala miliyan 180.
Kungiyar farfado da Tattalin Arzikin kasashen yammacin nahiyar Afirka watau ECOWAS ce, ta ba da umarnin kakaba wa kasar takunkumin, bayan da shugabannin sojin Mali suka juya baya kan shirin gudanar da zabe, inda suka ce za su ci gaba da mulki har na tsawon shekaru biyar.
Hukumomin Mali sun ce takunkuman, da kuma yanke tallafin da kasashen waje ke bai wa kasar, ya saba wa Ka’ida, kuma zai jefa al’umar kasar cikin matsanancin talauci.