Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jajantawa iyalan mutane biyar da suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama a Damaturu babban birnin jihar.
Gwamna Buni ya ce abin bakin ciki ne a rasa wadanda abin ya shafa a wannan mummunan iftila’in, amma wannan lokaci ne da Allah Madaukakin Sarki ya kaddara.
Ya kuma jajanta wa wadanda suka samu raunuka, ya kuma yi addu’ar Allah ya basu lafiya.
Gwamnan wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da takaici, ya ce Lamarin ikon Allah ne.
“Muna rokon Allah (SWT) ya gafarta musu kurakurensu, ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin,” Buni ya yi addu’a.
Ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta tabbatar da kula da wadanda suka samu raunuka tare da samar da kayan agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa domin rage musu wahalhalu.
Idan dai za a iya tunawa mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da jikkata wasu da dama a ranar Litinin da ta gabata sakamakon mamakon ruwan sama da tsawa da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.
Comments 1