By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 41 suka samu raunuka daban-daban a ranar Litinin din da ta gabata, yanzu haka an kwantar da su a Asibitin kwararru da ke Damaturu Jihar Yobe sakamakon mamakon ruwan sama da kuma tsawa.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) Dokta Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a Damaturu a ranar Talata.
Matasa Sun Zama Saniyar Ware Saboda Tsadar Fom Din Takarar Da APC Da PDP Suka Sanya — Yiaga Africa
A cewar sa “SEMA ta mayar da martani ga wadanda ginin ya rufta saboda tsananin iska da ruwan sama da aka asamu”.
“Tawagar bincike da aikin ceto ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe SEMA a ranar 9 ga watan Mayu, 2022 ta amsa kiran gaggawa daga al’umomin yankin da abin ya shafa.
Hukumar tace ta aike da tawagar jami’an ta don tallafawa wajen kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe.”
Goje ya bayyana cewa “jimillar wadanda abin ya shafa 41 sun fito ne daga al’ummomi/da yan kuna daban-daban guda 6.
A cewar sa yankunan sun hada, Waziri Ibrahim, unguwar Abbari, NayiNawa, Pompomari, Sai rukunin gidajen ‘yan majalissu, kan titin Gujba da kuma Maisandari.
Kazalika yace abin takaici mutane 5 sun mutu maza 2, mace babba 1, da kuma ‘yan mata guda 2.