Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya tabbatar da kudirin Gwamnatin sa wajen gyarawa da Samar da tituna a yankin Farm Centre don kara bunkasa harkokin kasuwanci a yankin.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Hukumar Gudanarwa na Otel din Bristol Palace Karkashin jagorancin mamallakin sa, Sanata Ibrahim Ida (Sardaunan Katsina) a Ofishin gwamnan dake Gidan Gwamnati.

Gwamnan ya sanar da cewar Gwamnatin sa tana aiki tukuru tare da Gwamnatin Tarayya wajen inganta wutar lantarki ta hanyar madatsun ruwa na Tiga da Challawa duk dai domin bunkasar kasuwanci a Jihar Kano.
Tun da farko Shugaban Hukumar Gudanarwar na Bristol Palace Sanata Ibrahim Ida, ya yabawa Gwamnan bisa kokarin sa na Samar da ingattaccen tsaro da kwanciyar hankali a Kano Wanda hakan ya baiwa masu harkokin Otel damar yin kasuwancin su cikin lumana.
Sardaunan Katsina ya kara da yin kira ga Gwamnan da yayi burus da masu adawa bisa irin ayyukan raya kasa da cigaban al’umma da yake yi a fadin Jihar Kano inda yace babu wata nasara da take tabbata ba tare da mahassada ba.
Daga karshe Gwamnan ya yaba masa bisa yadda yayi kokarin samar da otel din ya yake gogayya da manyan hotel na duniya inda yace hakan zai baiwa baki daga sassan duniya damar zuwa su zauna cikin natsuwa.
Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Hon. Ali Haruna Makoda; Mai baiwa Gwamnan shawara a kan harkokin masarautu, Alhaji Tijjani Mailafiya; kwamishinoni da sauran jami’an Gwamnati.