By Abbas Yakubu Yaura
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jos-ta kudu da Jos-ta gabas a majalisar wakilai, Dachung Bagos, ya bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da kuma kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, domin shiga tsakani a rikicin daya barke a majalisar dokokin jihar Filato.
Bagos ya bayyana zargin tsige shugaban majalisar, Ayuba Abok da cewa ya sabawa doka, inda yace mambobi shida ba su zama kashi biyu bisa uku na mambobin majalisar 24 ba, wanda doka ta tanada wajen tsige shi.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ‘yan majalisa takwas daga cikin 24 sun aiwatar da tsigewar ne a harabar majalisar a ranar Alhamis.
Abok, wanda ya zama dan majalisa na farko mai wakiltar mazabar Jos-maso-gabas, nan take aka maye gurbinsa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Pengana, Yakubu Sanda, na jam’iyyar APC.
Bagos, yayin da yake mayar da martani kan wannan ci gaban a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, yace an tsige kangaroo ne.sannan yace mutanen Filato zasu ci gaba da amincewa da Abok a matsayin Shugaban Majalisar.
Kazalika Bagos yaci gaba da cewa, “Yanzu ya zama dan akida saboda yana tsaye da jama’a sakamakon kashe-kashen da ake fama da shi da rashin tsaro a jihar, yana mai cewa a halin da ake ciki, yana bayar da bayanai kan hakikanin abin dake faruwa a Filato da kokarin samar da mafita a matsayinsa na shugaban majalisar da sauran ‘yan majalisar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “ jihar Filato tana da ‘yan majalisar wakilai 24 wadanda aka zaba kuma suke aiki.
Acewar Bagos mambobi shida za su zauna su yi juyin mulki da sunan tsige shi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.“Mambobi shida ba za su iyaba ta kowace hanya su zama kashi biyu bisa uku na ‘yan majalissa 24.
Comments 1