Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester City karon farko cikin wasa shida da ta buga a Firimiyar Ingila ba tare da rashin nasara ba.
Man City ba ta yi kama da kungiyar da Pep Guadiola yake jagoranta ba a daren yau ganin irin yadda ta kasa shafa kwallo kamar yadda aka saba.
Kashi 46.74% da Man City ta samu na rike kwallo a yau shi ne mafi karanci da Guadiola ya taba samu a matsayin mai horaswa. Hakan yana nufin Chelsea ta nuna bajinta duk da cewa tawagar Lampard din ba ta iya farke kwallo ta biyu da Mahrez ya ci a minti na 37 ba.
Amma dai ko ba komai City ta farfado daga kashin da ta sha a hannun Liverpool mako biyu da suka gabata da ci 3-1.
Ngolo kante ne ya fara bude wasan da kwallonsa mai matukar kyau minti 21 da take wasa, kafin daga baya De Bruyne ya farke ta a minti na 29.
Raheem Sterling ya ci ta uku a minti na 93 amma na’urar VAR ta ce an yi satar gida kafin a saka kwallo a raga.
Sakamakon bai zo wa Chelsea da dadi ba domin kuwa ta koma matsayi na 4 a kasan City maimakon na uku da take kafin take wasan.
Ita kuwa Man City ta koma ta ukun da maki 28, maki tara ke nan tsakaninta da Liverpool wadda ke saman teburi.