Ƙungiyar ƙaallon ƙafa ta Manchester City ta sake jaddada aniyarta ta sake komawa neman shahararren ɗan wasan ƙasar Argentina kuma mai buga wasansa a Barcelona wato Leonel Messi.
Manchester City ta bayyana hakanne bayan da a watannin baya taso ta sayi Messi sakamakon furtawa da yayi zaibar Barcelona lokacin da Bayern Munich tayimusu dukan kawo wuƙa a wasan kusa dana ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai a kakar wasan data gabata.
A watan Janairu na sabuwar shekarar daza a shiga za a sake buɗe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa a nahiyar turai domin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa su sake yin garambawul na sayen ‘yan wasa.
Ayanzu dai ana yin rurumar yin zaɓe a birnin Catalonia na Barcelona wato zaɓen shugaban ƙungiyar biyo bayan Bortemeu daya sauka a kwanaki 10 da suka gabata. Shine ita Manchester City zatayi amfani da damar yin rurumar yin zaben domin sayen Messi sukawoshi zuwa Ingila wato gasar ajin Firimiya.