Akwai alamu na alƙaluma da masana suka fitar da suke nuni da cewar akwai yiwwuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United zata iya kasancewa cikin tsaka mai wuya a watannin Oktoba da Nuwamba wato daga yanzu zuwa wata biyu kenan, inda zasu shiga tsaka mai wuyar a wasannin gasanni daban-daban da suka haɗar da gasar zakarun nahiyar turai da gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila da kuma gasar League Cup.
Hakan ya biyo baya ne ganin yadda ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Manchester United zata buga wasu wasanni masu zafi wasannin da ka iya zamowa barazana game da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Manchester United duba da yadda suka fara fafata kakar wasa ta bana da rangal-tangal.
Kusan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa tayi cefane wajen sayen ‘yan wasa musamman a ƙasar Ingila amma kuma Manchester United batayi wata siyayya daya dace ba duba da cewar ya kamata ta sayi manyan ‘yan wasa kamar guda shida amma kuma kwata-kwata guda 1 ta saya wato Van der Beek daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ajax, amma kuma ta nemi ‘yan wasa da dama a kakar wasa ta bana sai dai ta gaza sayensu inda daga cikin ‘yan wasan data nema tuni wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan suka rigasu.
Ana ganin matsalolin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United bazai wuce sayen ‘yan wasan gaba da kuma ‘yan wasan baya duba da irin abin da ya faru akan wasan kusa dana ƙarshe daya faru a kakar wasan data gabata a gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai wato Europa League tsakanin Sevilla da Manchester, sannan kuma ga abin da ya faru a wasan mako na biyu a filin wasa na OldTraford tsakaninsu da Crystal Palace inda hakan ke nuni da cewar dole sai an sake sayo ‘yan wasan baya.
Sai dai dangane da maganar sayen ɗanwasan gaba mai wayo duba da cewar yarinta tana damun ‘yan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, amma kuma a halin yanzu Manchester United tana tattaunawa da shahararren ɗan wasan gaba na ƙasar Uruguay wato Edison Cavani inda ake sa ran zasu kammala yarjejeniya dashi a wannan yammaci na Lahadi.
Dangane da jerin matsalar da Manchester United zata shiga na wasu wasanni masu zafi a watan Oktoba da Nuwamba, ga jerin Manyan wasannin da zata buga:
1. Ranar 20 ga watan Oktoba Paris Saint Germain zata fafata da Manchester United a wasan rukuni na gasar zakarun nahiyar turai.
2. A ranar 24 ga watan Oktoba Manchester United zata fafata da Chelsea a gasar Firimiya.
3. A ranar 28 ga watan Oktoba Manchester United zata kara da RB Liepzig a filin wasa na OldTraford a gasar zakarun turai.
4. A ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2020 Manchester zata kara da Arsenal a wasan gasar ajin Firimiya.
5. A ranar 8 ga watan na Nuwamba kuma Manchester United zata fafata da Everton.
Ganin cewar Manchester United zata fafata wasannin na masu zafi a jere ake ganin cewar rashin siyayyar da basuyi ba zai iya jawowa a ragargajesu sosai ganin cewar dukkanin wasannin masu zafi ne kuma komai zai iya faruwa duba da cewar a jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da Manchester United zata fafata wasanni dasu kowacce tayi siyayya sosai da sosai inda wasu kuma daman suna da isassun ‘yan wasa kamar Paris Saint Germain da RB Leipzig.
Manchester United dai tun bayan da tsohon mai horas warsu wato Sir Alex Perguson ya ajiye aikinsa har yanzu basu koma dai-dai ba inda a halin yanzu lashe kofi yake gagararsu inda ake ganin cewar gasar ajin Firimiya ta gagaresu duba da yadda aka sami ‘yan bana bakwai a wannan sabuwar kakar wasan da aka fara ta 2020 zuwa 2021.