Yan majalisun Jahar Nasarawa sun gayyaci Manajan Access Bank domin ya zo yayi cikakken bayani kan rashin biyan ma’aikatan Ilimi albashinsu. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Shugaban Yan majalisu masu rinjaye, Daniel Ogazi, ya bayyana haka a lokacin da Muhammad Dan’azumi yake bayanin kundin kasafin ayyuka na 2021 a majalisa dake Lafiya.
Yan majalisun Kuma, sunyi Kira ga hukumar Ilimi ta Jahar da su yi cikakken bincike kan yawaita makarantun kudi dake Jahar don tabbatar da ingancinsu.
KARANTA:- Daukar Jami’an Ƴan Sanda 400.000 Ba Gaskiya bane – Dingyaɗi.
Daniel Ogazi, yace dayawa daga cikin ma’aikatan sun karbi bashi sannan kuma zasu biya kudin ruwa kaso ashirin cikin kudin, banda kuma hauhawan farashin kayan ayyuka dake karuwa yau da kullun.
Halin da bankin ta yi na rashin biyan ma’aikatan kudadensu ya janyowa Jahar wani abun kunya a idon duniya, wanda kuma ta yi hakan ne akan wani dalili da ba’a san shiba, sun ajiye kudaden mutane suna samun riba daga garesu. Ba tare da izinin gwamnati ko jama’ar jahar ba.
“A dai jaha mun baiwa ma’aikatan hakkinsu, an sanya kudaden a banki, a lokacin da su kuma suka ki baiwa jama’a hakkinsu, sun sanya su cikin wani hali na daban.”