Manchester City ta sake daukar wani babban mataki na ci gaba da rike kofin gasar Premier yayin da kwarin gwiwar Kevin De Bruyne ya Bai wa kungiyar nasara a kan Chelsea da ci 1-0, inda ta baiwa Chelsea maki 13 a saman teburin.
Dan kasar Belgium din ya samu damar bai wa Manchester City nasaran ne yayin da wasan ya rage saura minti 20 a tashi, Wanda ya zura kwallo daya tilo da Kungiyar ta ci, Wanda hakan ya Bata damar lashe wasanni 12 a jere.