Kwallon da dan wasan Borussia Dortmund Marco Reus ya zura jiya shine Ƙwallo ɗaya tilo da aka ci Manchester City cikin Minti 790, Kwatankwacin Wasa 8 Kenan ba tare da an zura mata kwallo ba.
Kungiya ɗaya tilo da ta Kafa tarihin da ya fi wannan wanda kuma har yau babu Kungiya ɗaya da ta taba yin haka ita ce Arsenal.
Arsenal ta buga minti 995 ba tare da an zura mata kwallo ba a shekarar 2005 zuwa 2006, kwatankwacin wasa 12 Kenan ba a zura mata kwallo ba a Champions League.
Tarihin da har yau aka rasa samun Ƙungiyar da za ta karya.
Kazalika gabannin wanchan Shekarar ce Arsenal ta ɗauki gasar Firimiyar Ingila ba tare da an doke ta ba ko sau ɗaya.
Shi ma tarihi ne da a duniya har babu ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa da ta goge shi.