Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United da takwarar ta ta Chelsea na daga cikin manyan kungiyioyi biyar dake rububin ganin sun dauko dan wasan Mancehster city Sergio Aguero
A karshen Kakar nan ne dai kwantiragin sa zai kare da City bayan shafe shekara goma yana murza mata leda.
Har kawo yanzu dai babu takamaiman alkiblar dan wasa ina ta dosa, to sai dai ana lakanta shi da komawa kasar Spaniya ko kuma Italiya don sake sabuwar rayuwa.
A cewar wata jaridar kasar Faransa Foot Mercato dan wasan ka iya ci gaba da zama a Ingila inda tuni Manchester Unidted da Chelsea suka nuna shaawar su.
Kazalika Paris St. Germain ta kasar Faransa da Inter Milan ta kasar Italiya dukkanin su sun bayyana maitar su kan dan wasan.
Aguero wanda ya ci kwallaye 257 cikin wasanni 384 da ya fafata a city har yanzu bai bayyana alkiblar shi ba kawo yanzu.