Manchester United ta sanya ranar kammala cinikin Frankie de Jong daga Barcelona.
Kungiyar Red Devils suna da niyyar kammala komai game da cinikin dan wasan nan da ranar 30 ga watan Yunin shekarar nan, kammar yadda kafar yada labarai , ta TalkSPORT ta ruwaito.
Kungiyar Erik ten Hag na gab da cimma yarjejeniya da Barcelona kan dan wasan na Holland a kan kudi fan miliyan 68.
De Jong ba baƙo bane ga Ten Hag, tare da ‘yan wasan biyu sun yi aiki tare a Ajax kafin ɗan wasan ya koma Barcelona a 2019.
Sai da kungiyoyin biyu sun dauki lokaci kadan suna tattaunawa kan farashin da Barcelona ta sanya wa dan wasan.
Red Devils za su yi fatan cewa zuwan De Jong zai haifar da ɗimbin yarjejeniyoyin don samun sabbin fuskoki a kungiyar gabanin sabuwar kakar wasa.