Kocin Manchester United, Erik ten Hag, ya shirya tsaf kan neman aro dan wasan kungiyar Kwlalon kafa ta Chelsea wato Christian Pulisic , in ji ESPN.
Daily Post ta ruwaito cewa, Blues na tsammanin dan wasan na Amurka zai bar Stamford Bridge a kasuwar musayar ‘yan wasa na watan Janairu.
KARANTA WANNAN LAABRIN: Hadimin Buhari Ya Yi Murna Da Wani Babban Rashi da Kwankwaso Ya Yi a Jam’iyyar NNPP
United, Newcastle da Arsenal duk suna duba yuwuwar daukan Pulisic.
Wakilan Pulisic a shirye suke su nemo masa sabon kungiyar, shekaru hudu bayan ya koma Chelsea a kan fan miliyan 58 daga Borussia Dortmund.
Ten Hag na neman ya kara karfin kungiyar, bayan United ta soke kwantiragin Cristiano Ronaldo a makon da ya gabata.
Dan wasan mai shekaru 24 a yanzu haka yana wakiltar Amurka a gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.
A wani labarin kuma, Yan sanda Sun Ceto Jariri Da Wasu Yammata A Jihar Zamfara
‘Yan sanda a Zamfara sun ceto mata shida da dan shekara daya da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya bayyana haka a garin Gusau a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce masu garkuwa da mutane sun kama mutanen a kauyen Kadamutsa da ke karamar hukumar Zurmi a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar nan