Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ware zunzurutun kudi har pam miliyan 50 don dauko dan wasan baya na Real Madrid Rafael Varane, kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.
Kazalika dai Manchester United din ta nuna sha’awar ta kan dan wasan baya na Sevilla Jules Kounde mau shekara 22 wanda takwara ne ga Varane a kasar Faransa.
A daya hannun kuma Manchester City ta kara matsa kaimi kan dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane mai shekara 27 da kuma dan wasan tsakiya na Aston Villa Jack Greelish, cewar jaridar Sun.
Ita kuwa Borussia Dortmund na son yiwa Liverpool hawan ƙawara ne game da dan wasan PSV Eindhoven kuma dan kasar Holand Donyell Malen.
Dortmund na kokarin cike giɓin dan wasan da ta siyarwa Manchester United Jadon Sancho mai shekara 21 kamar yadda dan jarida Fabrizio Romano ya sanar a shafin twitter.
Har yanzu a hada-hadar yan wasan, West Ham United ta kasar Birtaniya ta kwallafa ranta kan dan wasan gaba na Liverpool Alex Oxlade-chamberlain idan ta gaza daukar san wasan Brazil Matheus Pereira, in ji Jaridar Express.