Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United dake ƙasar Ingila wadda take fafata gasar ajin Firimiya da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 20 suke haɗuwa su fafata a tsakaninsu ta maimaita wani mummunan tarihi data taɓa kafawa a kakar wasa ta 1972 zuwa 1973.
Ta sake mai maita wannan mummunan tarihinne bayan ta buga kunnen doki da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a wasan mako na shida na gasar ta ajin Firimiyar ƙasar Ingila a filin wasa na Old Trafford dake birnin Manchester.
Wannan mummunan tarihi shine Manchester United ta buga wasanni uku a jere a filin wasa na Old Trafford batare da tayi nasara koda a wasa guda ɗaya ba amma a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila wato sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.
Idan ba a manta ba wasan da Manchester United ta buga na farko tayi rashin nasara a hannun Crystal Palace. Sannan a wasanta na biyu a gida Tottenham ta lallasa ta daci 6 da 1. A yammacin Asabar kuma ta buga kunnen doki a wasanta na uku a gida da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea.
Rabon da Manchester United ta kafa irin wannan mummunan tarihi tun a kakar wasa ta 1972 zuwa 1973, sai dai ta sake kafa mummunan tarihinne a ƙarƙashin mai horas wa Ole Gunner Solksjaer wanda hanzu ya shiga kakar wasa ta 4 a matsayinsa na mai horas da Manchester United.