Manchester United mika tayin dauka danwasa Christian Eriksen idan kwantiraginshi ya kare. in ji jaridar The Athletic.
Eriksen zai zama dan wasan da bashi da kwantiragi a Brentford ranar 30 ga watan Yuni kuma sabon kocin United Erik ten Hag ya ce yana sha’awar yadda dan wasan ke taka leda.
Ten Hag yana kallon tsohon abokin wasan a Ajax, Frenkie de Jong, a matsayin babban burinsa, amma zai yi farin cikin idan Eriksen mai shekaru 30 ya sanya hannu a matsayin madadin zabinsa
Eriksen ya sami bugun zuciya a lokacin gasar Euro 2020, amma ya fara dawowar tamaula tare da Brentford a watan Janairu.
A kakar wasan da aka kammala, ya zura kwallo a raga kuma ya yi taimaka an ci hudu a wasanni 11 da ya buga don taimakawa kungiyar ta ci gaba da zama a mataki na gaba a gasar ta Firimiya.
United ta ci gaba da bin diddigin ci gaban Eriksen kuma an ba da rahoton cewa sun yi farin ciki da abin da suka gani dangane da takarawar dan wasan.