Manchester United za ta biya fam miliyan 41.8 ga Red Bull Salzburg kan Benjamin Sesko, kamar yadda Jaridar Sport ruwaito.
Sesko, mai shekaru 19, ya fito a matsayin babban burin kocin Man United Erik ten Hag a karshen kakar kasuwar musayar ‘yan wasa.
Shugaban kula da harkokin kwallon kafa na Man United, John Murtough kwanan nan ya tashi don tattaunawa da wakilin dan wasan saboda yana da sha’awar sayo dan wasan a matsyin na hudu da Ten Hag ya kawo kungiyar kafin rufe kasuwar cini kayyar yan wasa na bazara a ranar 1 ga Satumba.
Man United na shirin shiga gasar cin kofin Premier ranar Lahadi tare da kungiyar kwallon kafa ta Brighton.
‘Yan Bindiga Sun Sace Yara 3 A Jihar Kogi, Sun Bukaci Naira Miliyan 100
Edinson Cavani ya bar Old Trafford, Mason Greenwood bai samu damar dawowa wassani ba, kuma Anthony Martial ya samu rauni wanda zai hana shi buga karawar Brighton.
Hakanan ana alakanta Man United da Sesko a daidai lokacin da makomar Cristiano Ronaldo ta ke cikin rashin tabbas, inda kyaftin din Portugal din ke son komawa kungiyar da za ta iya ba damar sake lashe gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa ta bana.
A wani labarin kuma na daban.
Kwamishinan kasuwanci na jihar Jigawa, Salisu Zakar ya rasu
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Jigawa Salisu Zakar ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwalu Danladi Sankara ne ya tabbatar da rasuwarsa.
Ya ce, “A cikin karfin zuciya muke sanar da rasuwar dan majalisar zartarwa ta jihar Jigawa, Salisu Zakar, kwamishinan kasuwanci da masana’antu.
Kafin rasuwarsa, Salisu Zakar ya yi aiki a jihar Jigawa a wurare daban-daban, tun daga ma’aikacin gwamnati, ya zama shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (SUBEB), sannan kuma ya zama kwamishinan kasuwanci da masana’antu.
Ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano, da ke jihar Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekara 60 kuma ya bar matansa da ’ya’yansa da jikokinsa